Ban Kaunaceta Saboda Kyawunta Ba Ina Sonta Ne Saboda Wadannan Dalilai.

Wani mutum ya auri matar da yake ƙauna. Yana matuƙar ƙaunar ta suna zaman lafiya. Watarana sai ta wayi gari da wani ciwo ya feso mata a fatar jikin ta gaba ɗaya. A hankali ciwo duk ya mamaye ko ina a jikin ta. Har ya zama na kyaunta duk ya dishashe....


Ana haka watarana mutumin sai ya tafi cirani. A hanyar shi na dawowa gida, sai ya gamu da hatsarin mota wanda hakan ya sa ya daina gani....


Ammana dukda hakan rayuwar auren su ya ci gaba kamar yadda yake a baya.... Ana nan ana nan kyaun nata duk ya gushe, ammana makahon mijin nata bai ma san da hakan ba domin babu wani koma baya a rayuwar auren su saboda yadda yake matuƙar ƙaunar ta.


Ana haka Watarana sai matar ta mutu. Mutuwar ta ta ta sanya shi cikin ƙunci sosai. Bayan an gama zaman makoki, sai mijin ya ƙuduri aniyar zai bar garin. Sai wani mutum daga bayan shi ya ƙira Shi Yace dashi: "Yanzu Yaya zakayi kana tafiya kai kaɗai? Duk wannan tsawon shekaru matar ka ce take taimaka maka wajen tafiya?". Sai yace dashi: "Ba makaho bane ni, I kawai pretending na ke yi saboda idan ta san zan iya kallon cutar dake jikin ta, hakan zai fi mata ƙuna sama da cutar dake jikin ta. Ban ƙaunace ta saboda kyaunta ba kawai, a'a hasalima saboda halayen ta da dabi'un ta kyawawa na ƙaunace ta, shiyasa na zama makahon gangan domin sanya ta farin ciki".......


Ƴan'uwa masu daraja, idan muna ƙaunar mutum ƙauna ta Haƙiƙa, zamu kai matuƙar ƙurewa domin sanya su farin ciki, hakan kuma wani lokacin dole mu zamto tamkar makafi domin kawar da kai daga aibun wassu domin sanya su farin ciki. Kyau yana gushewa, ammana zuciya da ruhi koda yaushe ɗaya ne. Mu ƙaunaci juna ba don Kyawun halitta zalla ba, mu haɗa da kyaun halaye da dabi'u.


Allah Ya mana jagora ☺️ ☺️ ☺️ ☺️

0 Comments