Yadda Zaka Gane Fake Alert Akama Amaimakon Na Gaskiya.


Zaka Iya Danna Kan Hoton Dake Kasa Domin Karanta Wani Labarin.

👇👇👇

Assalamu Alaikum Jama'a Barkanmu Da Wannan Lokacin Sannunmu Da Sake Kasan Cewa Daku Acikin Shafinmu Mai Albarka.


A cikin kwana 2 nan na samu tambayoyi akan taya ake gane fake alert, to ga amsar masu tambaya game da fake alert.



Yan'uwa mu lura da kyau domin a irin wannan lokacin da muke ciki ne ya kamata musan hanyoyin kare kanmu, musamman 'yan kasuwa masu cinikayya da mutane daban-daban, dare da rana, kuma ma wasu mutanen baka sansu ba, kuma baka san inda suke ba bare idan suka cuceka ka iya gano inda suke.


Fake Alert ma'ana sa'ko tura ku'di na boge, wata hanya ce da 'yan damfara (scammers) suke amfani da ita wajen tura maka da sa'kon boge a matsayin sun tura maka ku'di alhalin babu abun da suka tura maka.



Mafi yawa anfi cutar al'ummar mu na arewa wa'danda suke da 'karancin sani akan irin wa'dannan hanyoyin da 'yan damfara (scammers) suke bi domin yaudarar mutane.


Akwai hanyoyi da dama da scammers suke amfani dasu wajen cutar mutun da sa'kon boge na ku'di (fake alert). Suna amfani da (fake sms) wanda za suyi ma kansu a matsayin bankinsu ne ya turo masu shi ta sanadiyar ya cire ku'din da suka turo maka, zasu amshi bayanan bankinka sai su tsara sa'kon daidai da yadda idan sun turo maka ku'di bankinsu zai turo masu da sa'kon, sai su turo maka da screenshot a matsayin shedarsu ta sun tura maka ku'di, idan kace masu baka gani ba, zasu ce maka ai zasu shigo matsalar network ne tunda su dai gashi har an cire masu ku'din daga bankinsu.



Lallai wannan hanyar ana amfani da ita wajen zaluntar mutanenmu sosai dan haka tabbas sai an lura sosai. Hanya mafi sau'ki wajen kauce ma wannan cutar shine: kada ka yarda an turo maka ku'di har sai kaga alert ya shigo maka ko kuma ka bincika 'kudinka dake asusun bankinka, shiyasa amfani da manhajar banki (bank app) ko ha'da email 'dinka da banki suke da matu'kar amfani, domin ta nan zaka iya dubawa idan ku'di na gaskiya sun shiga asusun bankinka.


Bayan haka akwai hanyar da suke bi su tura maka da sa'ko daidai da yadda bankinka suke turo maka sa'ko idan an turo maka da ku'di, wajen sunan mai turo sa'kon ne kawai suke chanjawa su saka sunan bankinka da ka basu a cikin bayanan bankinka, sai dai basa rubuta jimlar ragowar ku'din da suke cikin account 'dinka idan sun ha'du da wa'danda suka turo tunda basu san ko nawa kake dasu acikin asusun bankinka ba kafin suce maka sun turo, amma idan ka bari suka sani ta hanyar yi maka wata dabara tofa ka lashe.


Itama wannan hanyar suna amfani da ita sosai, abunda zai wayar maka dakai wajen gane cutarka akeso ayi shine: idan akwai sa'kon da bankinka sukayi maka a cikin jerin sa'konninka (sms) zaka ga wannan wanda mai niyar cutarka 'din ya turo maka ba'a cikin na bankinka yake ba, zaka ganshi daban shima na bankin naka daban. Idan kuma babu sa'kon da bankinka suka ta6a turo maka acikin wayarka to lallai hanyar da zaka bi dan ka banbance sai dai ka bincika ku'din da suke cikin asusunka na banki ta hanyar danna lambobin duba ku'di na bankinka ko ta hanyar manhajar bankinka (bank app) 


Haka kuma suna amfani da wasu hanyoyin da dama wa'danda sukafi wa'dannan dana gaya maku hatsari sosai, suma dai hanyar da zaka bi dan tsallakesu baya wuce ka tabbatar da 'kudi sun shiga asusun bankinka kafin ka amince da an turo maka da ku'di.



Zamanin da muke a ciki yanzu ya zama dole mutum ya nemi ilimin kare kanshi daga 'yan damfara (scammers) domin dare da rana cikin shiri suke da binciken hanyar da zasu bi domin su cuci mutane su tara ku'di. Allah ya kyauta.


Akwai hanyoyin sanin ilimin kariya daga 'yan damfara da dama da muke dasu, idan mutun yana son samun cikakken ilimin kariya a zamanance zai iya neman littafin CIKAKKIYAR KARIYA wanda shugaban Arewa Computer Library ya rubuta wato Salisu Abdurrazak Saheel  idan har ka karanta littafin tabbas zaka sha mamaki kuma zaka samu ilimin kariya sosai a zamance.



Anan Muka Kawo Muku Karshen Wannan Bayanin Kubuyomu A Sabon Shirin Nagaba Don Jin Wasu Bayanan Mungode.

0 Comments