Wasu Dabi'u Guda Uku ( 3 ) Dakan Iya Rabaka Da Budurwarka Har Abada.

Idan Ka Kasance Mai Aikata Wadannan Abubuwa Guda Uku To Babu Budurwar Da Zata Soka.


Danna Kan Wannan Hoton Domin Karanta Wannan Posting Din.

👇👇👇


Idan Kuma Bai Budeba Saika Danna Back Domin Karanta Wanda Ka Fara Karantawa.

👇👇👇


Assalamu Alaikum Barkanmu Da Wannan Lokaci Sannunmu Da Sake Saduwa Daku A Wannan Shafi Namu Mai Albarka.


A Cikin Darasin Namu Wanda Muke Masa Taken Ni Da Saurayina.


Zamu Kawo Muku Wasu Dabi'u Ko Halaye Da Yan'mata Suka Tsana Sosai Daga Bangaren Samari.


Kuma Ba Yan Mata Kadai Ba Hatta Samarin Sun Tsani Yan Mata Masu Irin Wadannan Dabi'u.


Saboda Haka Yana Da Kyau A Saurara Aji Wadannan Dabi'u Daya Bayan Daya Domin Kiyayewa Ta Yadda Za A Tafi Tare A Dawo Tare Wato A Gudu Tare Kuma A Dawo Tare.


Saiku Cigaba Da Karantawa A Nutse Domin Jin Wadannan Halaye Ko Dabiu Kamar Yadda Mukayi Bayani A Baya.


( 1 ) Kazanta.

Wannan Dabi'a Ko Ince Hali Yana Matukar Kauda Hankalin Yan Mata Daga Gareka Haka Itama Kazamar Budurwa Bata Burge Samari Duk Kyanta Kuwa.


Saboda Haka Yana Da Kyau Ki Kasance Mai Tsafta Kaima Ka Kasance Mai Tsafta Idan Har Kana Neman Soyayya Daga Yan Mata Da Kuma Sauran Al'umma.

Kai Kodama Soyayyar Ubangijinka Kake Nema Dole Saika Kasance Mai Tsafta Da Kula Da Kanka.


( 2 ) Abu Na Biyu Shine Rashin Cika Alkawari.


Yan'mata Basa Kaunar Saurayin Da Baiya Cika Alkwari.


Idan Akace Mutum Baya Cika Alkawari Kunga Yazama Makaryaci Kenan, Saboda Haka Rashin Cika Alkawari Alamace Ta Makaryata.


( 3 ) Girman Kai Wannan Alama Ko Dabi'a Itama Ko Kusa Bata Burge Yan'mata.



Domin Idan Mace Ta Fahimci Cewan Kai Mai Girman Kaine To Zata Fitane Daga Harkokinka.


Kai Bazama Ka Burge Wataba Barantana Ta Fara Mu'amala Dakai Koda Kuwa Akan Wani Abune Wanda Baikai Yakawo Ba.


To Haka A Bangaren Samari Suma Basa Kaunar Yan'mata Masu Ire-iren Wadannan Halaye.


A Karshe Muna Kira Da Fatan Dukkan Samari Ko Yan'mata Masu Irin Wadannan Halaye Da Dabi'u Zasu Gyara Su Daina.



Mungode Sai Munhadu Daku A Wani Sabon Darasin Anan Gaba, Inda Muke Fatan Zaku Kasance Da Wannan Shafi Namu A Kowane Lokaci.

0 Comments