Matakan Jawo Hankalin Saurayin Da Kike So Da Aure.

 


Matakan Jawo Hankalin Saurayin Da Kike So Da Aure.


'Yan mata da dama suna kamuwa da soyayyar samarin da basu masan suna yi ba. Wani lokacin ma samarin sun sani amma suna shakka ko tsoron soma furta kalaman soyayya ga irin wadannan matan.

Akwai Kuma lokacin da saurayin yasan budurwa tana son shi amma sam shi hankalinsa baya kanta. Don haka duk wani abunda zata ta yi na neman jawo hankalinsa baya samu. Idan kin samu kanki cikin irin wadannan matan da yanzu haka suke son saurayi amma sam shi bataki yake ba, to ga wasu dabarun da zaki bi domin ganin kin cimma burinsa na shawo kansa cikin sauki.

Sai dai kamin budurwa ta kwallafa rai akan son saurayi dole ne ta ajiye son rai a gefe ta yi nazari da tunanin ko wannan data ke so ya dace ya zama mijinta. Irin namijin da take fata da burin ta aura ne kodai kawai sonsa take babu hujja. Tabbas idan har ta gamsu shi wannan namiji ne da duk mace zata yi burin samu to daga wannan lokacin sai ta daura niyar ganin ta cimma burinta ta shawo kansa.

Irin wannan soyayya yana kasuwa ne kusan kashi hudu. Akwai namijin da kike so ya sanki kin sanshi. Akwai wanda kin sanshi amma shi bai sanki ba. Akwai kuma wanda kin san shi ya sanki amma baku taba haduwa ba. Akwai kuma wanda kece kika sanshi amma baki taba ganinsa ba. To duk wadanan ko wanne da irin yadda zaki shawo kansa. Yadda wasu dabarun da zaki yi amfani dasu a wancan a wannan bazai samu ba. 

Bari mu soma da shi namijin da kin sanshi ya sanki. Irin wadannan mazan basu da wahakar fadawa tarkon macen data san takunta. 

Kamin ki soma baza tarkon kamo irin wannan saurayi kiyi kokarin gano shi yana da wata macen da yake so ko take sonsa ko kuma suke soyayya. Idan kika samu amsar wadannan tambayoyin uku to kin samu Kashi 30 cikin dari na cimma burinki. 



Idan yana da wacce yake so, sai ki gano mai ya jawo hankalinsa akan ta har yake sonta. Idan Kuma wata ce ke sonsa sai ki natsu ki binciko ta hanyar da zaki datsaita. Idan kuwa soyayya yake yi da wata yi kokarin gano tsawon wani lokaci suke wannan soyayar, kuma menene matsayin soyayar tasu. Ki leko shi ko iyayensu sun aminta da wannan soyayar da suke yi ko suna fuskantar kalubale. Daga nan ne zaki fahimci zaki iya kwace ko kuma hakura zaki yi.


 


Idan kuma bai da budurwa nan ma aikin dake gabanki shine binciko mai hanashi yin budurwar, ya taba Yi da wata suka rabu ko bai taba ba. Kina samun amsar wadannan tambayoyin daga nan zaki sake share faggen daura damarar jawo hankalinsa gareki. 


Akwai saurayin da ya sanki kin san shi amma ko gaisuwa Baku taba yi ba kuma shi kike so. Akwai kuma wanda Kuna gaisawa daga nan babu kari. Nan ma kowanne cikinsu da yadda zaki shawo kansa.



Mu soma da wanda kunsan juna amma baku gaisawa kuma duk duniya nan babu wanda kike burin aure irinsa. To da farko kiyi kokarin samun shafukansa na sada zumunta ki aika masa sakon abota. Idan kika ga an kwana biyu bai karbi sakonki ba nan ma wata damace data sake samuwa a wajenki. A wannan yanayin kina da hujjar yi masa maganar cewa kin tura masa sakon neman abota amma bai karbeki ba. Kuma kinyi hakan ne saboda yadda kike ganin yana rubutu ko sharhi akan abunda kike ra'ayi wannan abun kuwa koda kwallon kafa ne abunda yafi rubutu akai shi zaki nuna masa kuna ra'ayin abu guda dashi.


Idan kuma kinyi sa'a a Kai tsaye ya karbi abotanki, to kada kiyi irin yadda wasu matan keyi sai suyi azarbabin turawa saurayin slm , yaya kake da zaran sunga ya karbi abotansu. Share kiyi kamar bakima san ya karbeki ba. 



Kiyi kokarin kina bibiyan duk wani rubutun da yayi kuka kima sharhi akai. Wani lokacin a wajen sharhin ki kalubalanci shi yadda zaku yi gardama ko kuma kiyi tambayar da zaki samu amsa daga gareshi.

 Hakan dabara ne na bude shafin samun kusantarsa cikin hikima.

Mataki na gaba kiyi kokarin gano wani yanayi na farin ciki ko bakin ciki da ya shafeshi yadda zaki masa jaje ko murna. Kuma a irin wannan yanayin kada ki masa gaba da gaba ko ta sakon sada zumunta. Ki yi kokarin samun lambarsa domin kiransa kai tsaye ki isar da sakonki. Muddin kika cimma wannan damar to akalla kin dau hanya.



Kin riga kin kulla wata alakar da zaku rika kula juna koda kuwa babu soyayya.

Da yake kunsan juna kuma har ma kuna magana a yanzu. To abu na gaba shine ki yi kokari duk lokacin da kuka hadu da shi kuka gaisa ki tabbatar da kin dauko wani hirar da bazaki bari ya yita da tsawo ba bare kuma a karasa ta. Kuna somawa sai ki datsai ki nuna sauri kike idan kuka sake haduwa zaku ci gaba. Kila yana da ra'ayin siyasa ne.



 Sai ki kalubalanci inda yake goyon baya yadda zai so kuyi magana akai amma kike kuma sai ki zulle. Wannan zai sa duk lokacin da kuka hadu da shi zai so kuyi hira akan kwantain maganganun da kuke dasu. Hakan kuma wata dama ce da kike kara jawo shi a jiki cikin mutunci da girmamawa ba tare da ya fahimci manufarki ba..

0 Comments