KALAMAN SOYAYYA MASU KARA DANKON SOYAYYA

                                         


KALAMAN SOYAYYA MASU KARA DANKON SOYAYYA

GA MASOYA Idan kana tare da budurwa masoyiyar ka, ya kasance kanayi mata kalamai masu dadi na jan hankali, wadanda zasu dinga faranta mata rai.

KAMAR HAKA

Na dade ina kallon taurarin samaniya yayinda naga wacce tafi kowacce haske, saina naga bakowa bace nike ganiba sai ke masoyiyata So gamon jinine, haqiqa sonki ya zamo jinin jikina Kinfita daban a cikin mata.


duk lokacin da na kallleki, sai naga kamar babu kyakykyawar wace sai ke Ki kwantar da hankalinki masoyiyata babu wata a zuciyata sai ke kadai Yarda da amincewarki gareni, sune zasu tabbatar da soyayyarki ta gaskiya a gareni.

Farin ciki baya dorewa a rayuwa sai tare da bakin ciki, dan haka kowane hali nike bazan ta6a mantawa dake ba masoyiyata Nakan raba dare ina mai roqon Allah don neman biyan buqata,

kKamar yadda kowacce bishiya kanyi rassa a sama, kuma tayi saiwa a qasa, haka sonki ya mamaye dukkan jikina.

KALAMAN SOYAYYA


Ina ma a ce na kasance da ke a duk bugun numfashina, kaunarki ce take kara tasiri a ruhina, babban burina na ga bayyanar fitar murmushinki a kan wannan kyakykyawar fuskarki, ya kuma zamana ni ne sanadin hakan. Bana son Allah ya kawo lokacin da za ki fushi da ni sosai kaina ba zai dauka ba, hakika Allah ya wadata ki da abin da mata da yawa suke nema sun rasa ke kanki kin san a cikin jinsinku, mata irinku kadan ne da a ce na iya rubuta labari da a kan fuskarki zan rubuta littafi mai suna kyauta daga Allah, kuma na san zan samu bayanan rubutu kamar guda uku 1,2 da 
Sararin samaniya na cike da taurari, teku na cike da ruwa, doran kasa na cike da ciyayi, amma ni zuciyata cike take da soyayyarki ba ta gushewa kamar yadda taurari ba sa gushewa a sararin samaniya, ba ta kafe wa kamar yadda teku ba ta kafe wa, haka zalika ba ta bushe wa kamar yadda ciyayi ba kamar sukan bushe, soyayyarki.



 dauwamammiya ce a farfajiyar madinan zuciyata da akwai wanda zai tsaga jikina da ya ga jininki yana gudana, a kan kaunarki na manta kaina, kikan hau ingarman doki domin ki taho mafarkina, wannan sunan da kika boye a tafin hannunki idan dare ya yi, ki duba sararin samaniya kin ga mai wannan sunan yana haska duniya masoyiyata, hakika na kasance mai bayyana a mafarkinki kin kasance a fatar lebena. Duk wani taku da na yi a doran duniya sai inji takun na iso ni zuwa gare ki. So marurun zuciya ya yi min saka tun asali so ya shige zuciyata yana min suka.
Ganinki burina, idanuwana ko bacci na farka ki amshi soyayyata abadan kada na koka ba ni barinki cikin kunci yaki zo na yi miki tarba. Daga motsin numfashina kika ziyarci rayuwata a matsayin abokiyar rayuwa a duk zantukana sai na ambace ki. Damuwarki kullum tana cikin tinanina ke ce jin dadina kuma ke ce bacin raina ke kadai ce a zuciyata kalamaina, zabina jin dadina, bacin raina, saboda da ke kawai nake rayuwata, kaunarki ce ke kula da ni take kuma kau da duk wata damuwa daga raina koda a ce babu ni ka san tuwata zan zamana a tare da ke har abada. Kamar yanda baki bai isa ya furta ba haka jiki bai isa ya nuna ba, sannan zuciya ta yi kadan ta kwatanta ruhinki ne kadai ya san yadda nake jinki a sakamakon ziyartar da yake yi wa ruhina a kowane dare ina sonki ba zan daina ba har abada saboda ban isa na daina ba.

Soyayyata da ke ba ta mutuwa kuma ba ta tsoran mutuwa koda za a yi mana kwace, ko da za mu mutu ko za mu lalace to soyayyar mu za ta kasance a raye na bayar da zuciyata na karbi ta ki na kamu da sonki. Ki tallafi rayuwata da ta tsunduma a kan tsananin soyayyarki, ki tausayawa zuciyar da ta shagala a kan tsananin soyayyarki ka da rintsi ko zugar mahassada ya sa ki guje ni ko kuma ki rage son da kike min, sonki yana dankare a zuciyata kamar yadda kwakwalwa ke dankare a kan dan’adam da a ce zan samu ikon fito miki da shi da na yi domin ki kara gazgata tsananin kaunar da nake miki.



KALAMAN SOYAYYA MASU SANYA MASOYA MURMUSHI


TA ‘DAYA. Ina son dukkan taurarin da suke bisan sama, amma ba za’a hada son da na ke yi musu da kuma na wadda ta ke a cikin idanuwan ki ba, in

0 Comments