Shin Ka San Wace Irin Mace Kake So A Ra'ayinka Kuwa.

 


Shin Ka San Wace Irin Mace Kake So A Ra'ayinka Kuwa.


Kuskure mafi girma da za kayi a rayuwar auren ka shine ka auri macen da ba irin ta kake so ba, kar ka taɓa yadda a ƙaƙaba maka wata yarinya ace wai ka aure ta matuƙar dai bata cikin irin jerin matan da kake so, idan kuwa har kayi gangancin yin haka to ba lallai ka samu natsuwa da jin dadi a gidan auren naka ba.



Kar ka taɓa yadda a yimaka katsalandan ko Shishigi wajen matar da zaka aura, saboda idan har kayi missing auren farko to Shikenan (Indai ba wani gyaran Allah ba) ka riga ka samu matsala a rayuwar ka.



Kowanne Namiji a duniya akwai irin abubuwan da yake so a wajen Mace, wani yafi son ƴar Lukuta wani kuma Muciya da Zani, wani fara wani baƙa, wani Doguwa wani gajeriya, da dai sauran wasu Features a jilin macen, to Amma su Wasu mazan saboda tsabar Sha'awa sukan kasa iya tsayawa ma su bambance cewa shin ita wannan yarinyar da suke tare, 



Sha'awar ta suke ji ko kuwa a'a sonta suke yi ? Shin tana cikin irin matan da suke so a halitta da ɗabi'a ko kuwa bata ciki ? Saboda rashin sanin amsar waɗannan tambayoyin shi yake sanyawa kaga mutum da matar shi a gida amma kuma bai daina gane-ganen ƴan mata ba, ko kuma yana da Budurwar shi amma kullum cikin kalle-kallen wasu ƴan matan, kuma ba zai taɓa iya dainawa ba har Sai lokacin da ya auri irin wacce yake so a halittance da ɗabi'ance.



Don haka, ka zauna kq natsu ka shiga duniyar tunane da ƙwaƙwalwar ka, ka don ka gano shin Sha'awar ta kake ji, idan eh haka ne to idan ka aure ta lallai akwai matsala, don kuwa (mafi yawa) samari auren Shaawa suke yi, sai bayan kwana biyu ka samu abinda kake sha'awa sai kuma kaga tayi muni ka koma jin haushin ta.



0 Comments