Tofah Ana Wata Ga Wata: Neman Aure Ba Hauka Bane Inji Wata Santaleliyar Budurwa.


 

Tofah Ana Wata Ga Wata: Neman Aure Ba Hauka Bane Inji Wata Santaleliyar Budurwa.


Assalamu Alaikum Jama'a Barkanmu Da Wannan Lokacin Sannunmu Da Sake Kasan Cewa Daku Acikin Shafinmu Mai Albarka.


Nakan wuce naga yan mata a social media suna posting videos ko pictures, suna cewa suna neman miji ga wanda yake shaawar auren su. Wata sai kaga har gantsarewa take, ta turo kirji da baya, don nuna irin halittar da Allah yayi mata.


Yan uwa na mata wannan salon bazai taba kawo miki mijin aure ba. Sai dai ya kawo miki karnika da shazumamai masu neman matan banza. Kuma ki lura, sune suke miki comments irin su "You are hot, sexy, you are beautiful" da sauran su.


Zan baku leakage.


A fitra ko halitta irin ta dan adam. Duk abinda yake mai arha baya da daraja. Duk abinda yake a bayyane, baya da daraja. Duk abinda ake tallatashi, baya daraja sabida mai shi ya nuna yunwar sa wajen ganin wannan abu ya fita.


Yanzu muna 21st century ne. Maza sun kara wayo ba irin na da ba. Yanzu maza ko da yan iska daga cikin ku, idan suka tashi aure, yarinya suke samu wadda take salaha kuma kamammiya, ba irin na kan social media ba. Shi namiji idan yaso aure, uwa ta gari yake nemawa yayan sa, ba ballagaza ba. Duk macen da zata iya bayyana surar ta akan social media toh zai wuya ta iya rike amanar aure da ta yara. Da kin nuna kan ki, toh kowa yasan kin yi failing wannan test din.


Haka zalika, maza sun daina aure don jima'i kawai. Saboda duk dokin jikin ki da namiji zaiyi, baya wuce na shekara daya. The rest ya zama tarihi. So yanzu maza suna neman wife material ne, mace mai kyan hali, tarbiyya, da kuma sanin ya kamata, ilimin ki na addini da boko, iya girkin ki, iya tarairaya, girmama na gaba, killace kai a gida, rashin yawo da sauran su.


Idan ma so kike ki samu miji, to ga yadda zaki:


1. Ki tsaftace social media page din ki. Ya zamto cewa baki yin shirme. Saboda yanzu haka, kamar yadda ake zuwa unguwa ayi tambaya akan matun, haka ake zuwa social media page don ganin waye kai. Wata tun anan take faduwa. An fasa aure da yawa akan irin wannan.


2. Idan kinga wanda ya miki, kiyi masa DM. Kiyi introducing kan ka, ki kuma bashi background naki, ki gaya masa achievements naki, qualifications, da kuma irin kudurin da kike dashi na ganin kin gina family da rayuwar aure mai kyau. Sannan da kuma gaya masa irin kwarewa da kike da ita a kitchen, da wajen kula da gida. Kar ki sake kiyi zancen "The Other Room". Zaki saka masa zargi a zuciyar sa.


3. Ko kuma ki rika posting akan abubuwan da suka shafi aure, da kuma tallata qualities na mace ta gari da miji nagari. Ta haka ne wani zai noticing naki ya miki DM sai kawai kiga kun fara maganar aure.


4. Sannan babu laifi idan ki rubuta wani dan takaicencen background naki, ki bada a wani babban social media page kamar irun su Abis Fulani, Young Ustaz, Hausa Fulani, ko page na mu na Mufti Menk Motivational Moments mai mabiya Muslimi million daya. Sai ki roki alfarma ko ki bada dan wani abu a saka. Ace ga wata baiwar Allah tana neman abokin zama kuma miji na gari. Wallahi, da yawa sun yi aure ta wannan hanyar.


Yana da kyau ki sani. Ba faduwa bace ko wulakanci, don kin nemi namiji ya aure ki. Asalan ma, yana kara daga darajar ki ne. Kuma Allah yaga kokarin ki, tabbas zai sa miki hannu kuma ya kawo miki dauki. Kar kice kawai ai kina addua, wani lokacin sai mutum ya tashi tsaye bayan anyi adduar.


Muna addua ga kannan mu, da iyayen mu zawarawa, da kuma daukacin yan matan duniya da suke son aure da gaske, Allah ya aurar da ku, Allah ya baku maza nagari, Allah ya cire muku wannan damuwa taku, Allah ya kara muku hakuri. Amin.


Anan Muka Kawo Muku Karshen Wannan Bayanin Kubuyomu A Sabon Shirin Nagaba Don Jin Wasu Bayanan Mungode.

0 Comments