Labarin Wani Yaro Mai Matukar Sa,a A Rayuwa.

Labarin Wani Yaro Mai Sa,a.
Wata Rana Wani Yaro Ya Yanke Shawarar Barin Garinsu Domin Zuwa Fatauchi Tare Da Matarsa Suka Hada Kayansu Basu Tsaya Ako Inaba Sai A Wani Kauye Dage Nesa Dasu Kadan.
wani mutum da matarsa talauchi ya dameshi a
garin da yake sai ya tafi chirani wani gari mesuna
Zariya aka bashi masauki kuma akabashi gona
yayi noma, matarshi kuma sai ta fara sana'ar
wainar gero kuma tasamu karbuwa sosai.
Wata rana da baije gona ba da safe yana Daki a
kwance amma yana iya hango matarsa tana aikin
waina kuma yaga mutane anata zuwa siya harda
idan tabada chanji yana kallo, bayan ta gama ta
dawo daki tafito da kudin zata kirga sai yace
mata basaikin kirgaba kudin jaka biyune kuma
tana kirgawa sai taga hakane saita fara mamaki
ta fara cewa ashe mijinta Dan baiwa ne amma
yana boyewa kar mutane susani, yace mata shi
bahaka bane amma taki yarda. Duk inda taje
saita dinga fada cewa mijinta Danbaiwa ne.
Watarana akuyar makota ta bata sai aka garzayo
wajen Danbaiwa yace musu shifa baisan komaiba
amma matar tacemusu suje kawai ita zatai
magana dashi. washe gari da safe ya hau sama
zai gyara dakin sa saboda yana zuba idan ana
ruwan sama kawai saiya hango akuyar kamar
yadda aka siffanta ta achan bayan gari ta makale
chikin sarkakiya dayasakko yacewa matar ta fada
musu suje bayan gari chikin sarkakiya zasuga
akuyarsu. Aikuwa gari yadauka anata fadin
Danbaiwa. Ana chikin haka sai akasache zoben
sarki. Sarki yace a kirawo Danbaiwa da yazo ya
cewa sarki shifa baisan komaiba Sarki yace
bazaije ko Ina ba saiya bayyana masa Wanda ya
dauki zoben sa, aka bashi daki a gidan sarki
domin yaji dadin aikin har zuwa dare saiga daya
daga chikin matan sarki tazo saboda ta sami
labarin irin aikinsa. Tace dan Allah ya rufa mata
asiri ga zoben takawo yace mata ba komai taje
ta sakashi a waje kaza, gari na wayewa ya
fadawa sarki aje waje kaza za'a ga zoben. Farin
ciki ya kama sarki haryace zai nadashi limamin
garin.
Bayan yakoma gida hankalinshi a tashe saboda
yasan ko alwala ma bai iya sosai ba balle limanci
yanata shawara iri-iri ita kuwa matarshi saimurna
takeyi mijinta Danbaiwa yasami daukaka. Kawai
saiya yanke shawarar yayi shiga irin ta mahaukata
yadau sanda yaje Fada yarufe sarki da duka dan
ache ya haukace sai afasa nadashi limanci,
yashiga Fada tamkar mahaukaci yadaga sanda
yakaiwa sarki duka sai sarki ya kauce sai rawanin
sa ya fadi kasa nan take akaga macizai da
kunami a chiki. makiyan sarkinne suka saka
masa a chiki dan yamutu suhau sarautar nanfa
akayita murna cewa Danbaiwa ya kubutar da
sarki. hakanan dai aka nadashi limanci. Lokacin
sallar azahar yayi akace liman bisimillah ya shiga
Kama ruwa ya dade bai fito ba saboda su gaji su
fara sallah amma sai da suka jirashi ya fito, ya
fara alwala upside down suma duk suka yi tasu
alwalan sukace Ashe tuntuni ba daidai sukeyi ba
aka fara sallah sai da akayi ruku'u sai yayi
tunanin ya sulale ya fita dan suce ya haukace
sucireshi daga limanci. A durkushen ya fito ta
kofar liman sai ladan shima ya fito a durkushen
sai sarkima ya fito a durkushen sai na kusa da
shi, a haka saida kowa yafito na karshen yana fita
sai masallachin ya ruguje kasan ginin kasa idan
yasha Ruwa kuma akayi Rana, nanfa sukayi ta
murna Danbaiwa ya ceci al'umma.
Shin wai wacce shawara zaku bashi domin ya fita
daga chikin wannan chakwakiya??.

0 Comments