Littafin Ramin Mugunta Part (1)

Littafin Ramin Mugunta Littafi Na Daya Part (1)
Wadda Khaleesat Haydar Ta Rubuta.
kanta ta ce yanxu in sauri ne zan isa gida tunda
munyi sallama sai na ce Allah ya kiyaye yace oh
korata kike tace ba haka bane innaga ba
mutumcin mu bane ace mun mun tsaya a hanya
muna magana hakan zai zubar mana da mutuncin
mu da kimarmu yace hakane to she kean Allah ya
hada fuskokinmu da alheri tace Amin Ina maka
addu'at samun budi da daukaka a rayuwar ka
kuma Ina rokanka ka maida hankalinka akan abin
da yazamar maka wajibi ka sani na damka maka
amanar soyayyata zan rayu da Sonka ba zan taba
son waninka ba Zuciyata taka ce ni kuma bani da
burin da ya wuce na muna maka gatan da babu
namijin da zai samu irinsa Ashroup ya duba lallai
maganar daga bakin Kaleesat take fitowa yana
mamaki kwarai saboda tana da matukar kunya
da kamun kai shi zai iya bugar kirji yace duk cikin
unguwar babu yarinya mai kimar ta Ya ce
Kahleesat ni ke ce tawa Ina rokonki ki rike
alkawari saboda nasan cewa idan na rasa ki
tabbasa rayuwata zata shiga kunci domin na rasa
uwar ya'ya ta gari wacce kowanne mutum zai so
ya ajiye ta cikin gidansa Ta sanya hannu ta rufe
fuskar ta ta juya tace Allah ya sadamu da alheri
ya ce Amin Ta juya yana kallonta cikin shiga ta
kamala hijabinta har kasa iska na kada shi yaji
nishadi sosai domin yana tsananin son Kahleesat
A Umar
Gari na maiduguri hadari ya gangamo iska mai
mutukar karfi tana tsananin kadawa Umman
Kahleesat ta hada kayayyaki saboda ganin hadari
Haka maigida Alhaji Umar yana tayata domin shi
mutum ne mai mutukar kula da matarsa yana
taimakonka sosai shiyasa bata iya masa musu
komai Dan ta tabbatar shine cikin burin ta ma'ana
ya cika irin namijin da kowace mace zata so ace
mijinta ne
Sun kamala a dai dai lokacin Kahleesat da Yusif
suke shiga kowanne dauke da alkur'ani mai girma
Mama barka da gida tace yauwa ya ya kun shigo
Ya juya yace Baba ashe har ka dawo
Ya ce Eh yaran kirki kun iso Toh Allah yasawa
karatun naku albarka Allah yasa na tsoran Allah
ne suka Amsa da Ameen Yusif ya ajiye kur'aninsa
ya juya zuwa dakinsa yayin da Kahleesat ta cire
hijabinta itama ta ajiye lokacin ruwa ya goce
Alhaji Umar Tambai lan asalin garin maiduguri ne
mutumin kirki ne kwarai yana da Yayarsa Yakaka
wace mahaifiyarsa ta auri Babansa lokacin tana
karama wato dai uwarsu daya Yanada yayyu maza
da mata shi ne auta a gidansu gidan karatu ne
sosai ma'ana suna Boko suna islamiya Abin da
zai baka mamaki shi daya uwarsa ta haifa sauran
duk sunada yan'uwa dama babarsu biyu ta haifa
daga shi sai Hajiya Yakaka
Hajiya Yakaka tayi karatu mai zurfi kamar yadda
yayan Alhaji Umar suke ba zaka ce ba yar gidan
bace domin tun a boding school ta dauki izzu da
wayewa ta dorawa kanta abin da zai baka
mamaki kai kace yar wani ce domin akwai
kwakwalwa tana masifar Jin turanci iya ado
Mahaifiyarsu tayi kokarin ganin ta sauke ta akan
wannan halaiyar amma ina cikin ikon Allah. Allah
ya hada jininsu da Babban da gidan Alhaji
Tambai wato Abba amma asalin sunansa
Abubakar soyayya sukeyi sosai domin shi a waje
yayi karatu a yanxu furofesa ne yana jami'a
sokoto anyi bikin wayewa sunyi auren yanci sosai
duka yan Boko ne
Hajiya Yakaka tana cikin daula ita da mijinta da
'ya'yanta mace ce mara son zumunci bata da
kirki ko kadan watanta biyu da aure mahaifiyarta
ta rasu Maimakon ta dauki Umar ta rike amma ko
a jikinta ta shiga cikin yan dakin Pro Abba ta
hade kai da su duk da su ma ba dadinta sukeji
ba amma gwanda su Umar ya taso cikin wahala
da kyara har ya Allah yasa ya girma da kansa ya
gudu Maiduguri Dan ya samu sassauci
A nan yayi ta fadi tashi Dan ya sauka unguwar
Dambuwa road ya hadu da yaramasu tarbiya har
ya kuma ya zama dan anguwar A nan har yayi
University ya fito da sakamako mai kyau duk
Wanda Wanda yasan unguwar Dambuwa road ya
sansu da karam ci domin takensu zumunta Dan
unguwar

0 Comments