Maganin karin ni,ima da gamsar da maigida a lokacin saduwa.




Assalamu alaikum barkanmu da warhaka sannunmu da jimirin sake kasancewa da acikin wannan shafin namu metarun albarka.


   GYARAN JIKI


 Gyaran jiki abu ne mai matukar muhimmanci a rayuwa da zamantakewa ta dan adam. Kamar yadda yake a addini wajibi mutum ya kasance yana kula da tsaftar jiki, asali ma tsafta tana daga cikin cikar imani. 


 Gyara ko tsaftar jiki wajibi ne ga maza da mata amma zamu fi karkata shawarwarinmu zuwa bangaren mata saboda tsaftarsu tafi muhimmanci kasancewarsu abin kwalliya na duniya.


KARIN NI'IMA DA GAMSAR DA MAIGIDA:


 Zaki samu kankana ki markada a blender ki saka garin ridi aciki da madara da zuma ki zubawa oga yasha kisha.


KARIN NI'IMA DA GAMSAR DA MAIGIDA


 Kisamu kanumfari ki jika kirisha kina tsarki yana karin ni'ima da matse Gaban mace.


 KARIN NI'IMA DA GAMSAR DA MAIGIDA


 Karin sha'awa da juriya yayin saduwa.


 Danyen zogale zaki wanke ki markada shi kitace ruwan ki zuba garin kanumfari da madara da zuma kina sha safe da yamma.


 Wannan hadin yana Karawa mace ni’ima sosai.

 


SIFFOFIN MIJI NAGARI


   Darasi na Hudu-(4)


*IRIN MIJI DA KOWACCE MACE TAKESO MARSAYIN MIJIN AURE*


Kamar yadda ba kowacce Mace Namiji ke so ba haka zalika ba kowana Namiji Mace ke so ba.


Akwai wasu siffofin nagari dake tattare da Mijin da kowacce macce ke so:


1-Mijin dake son matarsa bayan aurensu fiyeda yadda yake sonta a layi.


2-Miji mai kishin matarsa.Domin Annabi Sallallahu alaihi wasallam yace: *(Duk wanda baya kishin matarsa bazai shiga Aljannah ba)*.


3-Mijin da ya dauki aure a matsayin Ibadah,ba wai abin wasa ba ko kuma abin jin dadin rayuwa kawai ba.


4-Wanda ya dauki matarsa a matsayin abokiyarsa, kanwarsa,almajirarsa,kuma abokiyar shawararsa.


5-Shine wanda baya zagin matarsa,baya cin mutuncinta,baya cin zalinta,baya ha’intarta koda a bayan idonta ne.


6-Shine wanda yake zaune da iyalinsa cikin amana da gaskiya da kyautatawa ba cuta ba cutarwa.Wanda idan ya fahimci halayen matarsa, yake hakurin zama da ita tare da kyautatawa domin neman rahamar Allah Ta’ala.


7-Shine wanda idan zai yi magana da matarsa, zai fadi gaskiya babu yaudara ko karya acikin zancensa.


8-Shine wanda ya dauka a zuciyarsa cewa: *Iyayen matarsa,Iyayensa ne. ‘Yan uwanta ma‘yan uwansa ne,kuma dangin matarsa danginsa ne*


9-Shine wanda yake daukar cewa farin cikin matarsa shine farin cikinsa kuma matsalar ta,itama tasa ce.


10-Shine wanda ke kokarin kiyaye sirrin matarsa,kuma yake kokarin kare mata mutuncinta koda a wajen ‘yan uwansa ne, tare da hikima da fahimtarwa.


11-Shine wanda baya fifita matarsa akan ‘yan uwansa,kuma baya tauye mata darajarta.Yana bawa kowanne gefe nasa hakkin kamar yadda shari’ah ta tanadar.


12-Shine wanda ya tanadi ruwan afuwa da hakuri a cikin zuciyarsa domin kashe wutar tashin hankali da bacin rai a duk lokacin da hakan ta faru tsakaninsa da matarsa.


13-Shine wanda a kullum yake kokarin tarbiyyantar da iyalinsa akan rayuwar addinin Islama ba rayuwa irin ta yahudu da nasara ba.


14-Shine wanda yake zaune da matarsa komai dadi komai wuya ba zai dena nuna mata soyayya ba wai don tafara yankwanewa ko kuma karfinta yafara raguwa.


15-Shine wanda yake bawa matarsa yabo a duk lokacin da tayi kwalliya ko kuma tayi girki komai rashin dadinshi.Miji nagari baya raki baya ihu don yaji abinci yayi yaji ko gishiri yayi yawa. Sai dai yace: *“uwargida abincin nan yayi dadi iyaka, sai dai gishiri yayi mana shisshigi a ciki”*


*Allah Yasa mazaje su gane,su sauke hakkinsu na Aure,  


Allah shine mafi sani.

0 Comments